Isa ga babban shafi

Najeriya: An ceto wasu daga dalibai mata da 'yan bindiga suka sace a Zamfara

A Najeriya, jami’an rundunar hadin gwiwa ta Operation Hadarin-Daji sun ceto dalibai mata shida na jami’ar tarayya dake Gusau a jihar Zamfara da wasu 'yan bindiga su ka sace da sanyin safiyar Juma’a.

'Yan bindiga na ci gaba da addabar mutane a yankin arewacin Najeriya.
'Yan bindiga na ci gaba da addabar mutane a yankin arewacin Najeriya. The Guardian Nigeria
Talla

Jami’in yada labarai na Rundunar, Operation Hadarin-Daji, Cpt. Ibrahim Yahaya, ya tabbatarwa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ta wayar tarho.

Da sanyin safiyar wannan Jumma'ar ce rahotanni daga jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya su ka ce ‘Yan bindiga sun kai hari tare kwashe dalibai mata masu tarin yawa a Jami'ar gwamnatin tarayya da ke Gusau.  

Bayanan da wakilin mu dake Sokoto Farouk Mohammad Yabo ya tattaro daga Sabon Gida inda dakunan kwanan daliban suke, na cewa gabanin Asubar yau Juma'a ‘yan ta'addar suka kai harin tare da kwashe daliban da kawo yanzu ba'a tantance yawansu ba.  

Kuna iya latsa alamar sauti domin sauraron rahoton Faruk Mohammad Yabo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.