Isa ga babban shafi

Kungiyar Boko Haram ta saki wasu mata 49 da ta yi garkuwa da su

Kungiyar Boko Haram ta saki wasu mata 49 da ta kama ta kuma yi garkuwa da su a jihar Borno dake arewa maso yammacin na Najeriya.

Kungiyar Boko Haram a wani taron mambobin ta
Kungiyar Boko Haram a wani taron mambobin ta AFP - HO
Talla

Matan sun samu samu shakar iskar ‘yancin ne a ranar juma’a da ta gabata bayan da jami’an jihar suka biya kudin fansa domin a karbo su.

Wasu mazauna yankin da suka bukaci a sakaye sunan su, sun tabbatar da an sace matan ne ga kamfanin dillancin labarun Reuters, a yayin da suke kan aiki a gona a kauyen Shuwaei kawuri da ke kewayen Maiduguri.

Daya daga cikin wadanda aka yi garkuwa dasu ta baiyana cewa ‘yan kungiyar ta Boko Haram sun shaida musu cewa sun sake su ne saboda biyan kudin fansa da ‘yan’uwansu suka yi.

‘yan kungiyar sun bukaci a biya su naira miliyan 3 da dubu dari 3 da 91 kafin a saki matan abinda ya sa jami’an jihar suka biya naira miliyan 1 kafin sakin su.

Mayakan boko haram sun dade su na garkuwa da mutane a jihar Borno domin karbar  kudin fansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.