Isa ga babban shafi

Nijar: Mayakan ISWAP na kwarara cikin Najeriya da Tafkin Chadi

Rahotanni na nuna cewa mayakan kungiyar ISWAP na barin sansanoninsu da ke yankin Sahel da Jamhuriyar Nijar, inda suke komawa wasu sassan yankin Tafkin Chadi da Arewa maso yammacin Najeriya.

Wasu daga cikin motocin da sojojin Najeriya suka kwato daga hannun mayakan Iswap
Wasu daga cikin motocin da sojojin Najeriya suka kwato daga hannun mayakan Iswap AUDU MARTE / AFP
Talla

Jaridar Daily Trust ta Najeriya ta ruwaito wata majiya mai karfi daga rundunar sojin kasar na cewa, yan ta’adda da yawansu cikin kungiya-kungiya na barin yankunan Sahel da manyan makamai.

Majiyar sirrin ta rundunar tsaron Najeriya ta kuma ci gaba da cewa mayakan na ISWAP na wannan hijira ne don guje wa abin da ka-je-ya-zo a shirye-shirye da kungiyar ECOWAS ke yi na afaka wa Nijar da yaki.

Majiyar tsaron ta kuma ci gaba da cewa akwai kwararran shaidun da ke cewa ‘yan ta’addar sun fara yada zango a yankunan Kukawa, Abadam, Gaidam da Guzamala garuruwan da ke kewaye da Tafkin Chadi.

Wasu daga cikin kungiyoyin ISWAP sun yada zango ne a jihohin Katsina, Kaduna Zamfara da Sokoto, dukkaninsu da ke arewacin Najeriya.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa tuni wannan ya fara barazana ga zaman lafiyar da aka fara samu a kewayen yankin Tafkin Chadi, sai dai kuma bayanai na cewa tuni dakarun Civilian JTF suka fara gyara dammararsu.

Cikin wadanda ake zargin sun yi hijirar daga yankin Saharar ta Jamhuriyar Nijar zuwa Tafkin Chadi har da Abubakar Modu, Sheikh Ba’ana Dujum, Marte Alwady, Muhammed Ibn Abubakar da kuma El-Mansur Dawahli Mouda dukkaninsu manyan kwamandoji a kungiyar ta ISWAP.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.