Manoma a Najeriya na korafi game da tsadar takin zamani
Manoman Najeriya na kokawa a kan hau hauhawar farashin takin noma, duk da samun yawaitar masu sarrafa shi a kasar.
Wallafawa ranar:
Farashin takin noman na karuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin kasar ta zuba sama da Dala miliyan 121 a wani Shirinta na samar da wadataccen taki.
Najeriya da ke da yawan manoman shinkafa da rake,yawancinsu tsadar taki ya haifar musu da matsaloli mabambanta wajen samun adadin da suke bukata na takin da za su yi amfani da shi wajen noma.
Yayin da wata manomiya Ajulo Mojisola ta ce wani bangare na gonarta ne kawai ta iya nomawa, saboda tsadar takin zamani.
Mojisola ta cigaba da cewa ta rage girman gonar ta ne saboda bazata iya siyan adadin takin da take bukata ba sabida tsadar sa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu