Isa ga babban shafi

Ba za mu yi wa Tinubu juyin mulki ba - Sojojin Najeriya

Rundunar Sojin Najeriya ta ce akwai makirce-makirce daga bangarori daban-daban na tunzura sojojin kasar domin su hambarar da gwamnatin dimokaradiyya da Shugaba Bola Tinubu ke jagoranta.

Shugaban kungiyar ECOWAS kuma shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu kenan.
Shugaban kungiyar ECOWAS kuma shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu kenan. AFP - KOLA SULAIMON
Talla

Sai dai ta ce yunkurin ba zai yi nasara ba, inda ta nanata cewa sojoji suna jin dadin kasancewa karkashin mulkin dimokuradiyya, don haka ba za su shiga duk wani mataki na yin zagon kasa ga dimokuradiyyar Najeriya da aka kafa, bayan kalubalen da kasar ta fuskanta.

Daraktan yada labarai na rundunar sojin kasar, Birgediya-Janar Tukur Gusau, wanda ya bayyana hakan a wani sakon da ya aikewa manema labarai a safiyar ranar Asabar, ya bayyana wannan jita-jita a matsayin rashin kishin kasa.

A cewarsa, sojoji za su ci gaba da gudanar da ayyukansu na tsarin mulkin kasar maimakon shirya duk wani juyin mulki ga gwamnatin dimokaradiyyar da ke tafiyar da ikon kasar a yanzu.

Martanin Gusau ya biyo bayan kiraye-kirayen da wasu ‘yan Najeriya suka yi na cewa sojoji su shiga cikin shugabancin kasar sakamakon gazawar gwamnatocin dimokaradiyya.

Haka zalika a cikin sakon nasa, babban hafsan sojan ya ce sojojin Najeriya karkashin jagorancin babban hafsan tsaron kasar,Janar Christopher Musa, ba za su shiga cikin kowane irin shiri na tayar da kayar baya ba ga Najeriya ba.

Ya kuma yi watsi da kalaman batanci da ake ta yadawa a wasu shafukan sada zumunta cewa ba a kula da dakarun sojin Najeriya yadda ya kamata, yana mai cewa ba za su bari wani mutum ko wasu mutane su tunzura jami’an soji kan gwamnati mai ci ba.

Sanarwar ta bayyana cewa, rundunar sojin kasar karkashin jagorancin babban hafsan hafsoshin tsaro, Janar CG Musa ta kuduri aniyar yin biyayya ga kundin tsarin mulki karkashin mai girma shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, kuma ba za ta shagaltu da ayyukanta da suka fayyace yadda ya kamata ba, kamar yadda kundin tsarin mulkin da aka yiwa kwaskwarima a 1999 ya ce.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.