Isa ga babban shafi

Majalisar wakilan Najeriya ta bukaci girke karin dakaru a iyakokin kasar

Majalisar wakilan Najeriya ta bukaci rundunar sojoji, ta tura karin dakaru don samar da tsaro a iyakar jihar Sokoto, domin kawo karshen amsar kudin da masu ikirarin jihadin kasashen Jamhuriyar Nijar da Mali da kuma Libya ke yi a hannun mazauna yankunan da ke kan iyakokin kasar. 

Wasu sojin Najeriya yayin rangadi.
Wasu sojin Najeriya yayin rangadi. AFP - AUDU MARTE
Talla

Dan majalisar da ke wakiltar mazabar Tangaza da Gudu na jihar Zamfara Sani Yakubu ne ya gabatar da kudiri a zauren majalisar, inda ya ce ‘yan ta’addan na amfani da dazukan Tsauna da kuma Kuyan Bana da dukkaninsu suka ratsa har cikin jamhuriyar Nijar, wajen aikata ta’addancinsu. 

A cewar dan Majalisar kungiyoyin ‘yan ta’addan da ke yankin da a baya basa ga maciji da juna a yanzu sun hade waje guda, inda suka sha alwashin hana ayyukan noma da kiwo, wanda ke matsayin sana’ar mutanen yankin, lamarin da kuma ke kara jefa rayuwar mutanen yankin cikin garari. 

Dan majalisar ya ce idan har ba a dauki matakan da suka kamata ba, hakan zai kara haddasa matsalar karanci abinci a sassan Najeriya, lura da gudunmawar da yankin ke bayarwa wajen samar da abinci a kasar. 

Wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da shugaban rundunar sojojin kasa na kasar, Manjo Janar Taoreed Lagbaja ya shaidawa gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal cewar dukkanin shirin afuwar da aka yi a kasar sun gaza cimma muradun da aka samar da su a karkashi, maimakon haka ma sake baiwa ‘yan ta’adda damar dunkulewa waje guda ya yi don kaiwa al’umma hari. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.