Isa ga babban shafi

Gwamnatin Najeriya ta ce babu abin da zai hana ta mulki ga Tinubu

Gwamnatin Najeriya, ta bada tabbacin cewa mika mulki daga shugaban kasa, Muhammadu Buhari zuwa ga zababben shugaban kasa, Bola Tinubu, zai kasance cikin kwanciyar hankali da lumana.

Sabon zababben shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu tare da shugaban kasar mai barin gado Muhammadu Buhari, lokacin da ya kai masa ziyara a gidansa da ke daura a jihar Katsina, ranar 01 ga watan Maris 2023.
Sabon zababben shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu tare da shugaban kasar mai barin gado Muhammadu Buhari, lokacin da ya kai masa ziyara a gidansa da ke daura a jihar Katsina, ranar 01 ga watan Maris 2023. © Presidency/BashirAhmad
Talla

Hakan dai ya zo ne kamar yadda gwamnati ta ce an kammala gyaran ofisoshi na shugaban kasa da mataimakin shugaban kasa.

Da yake jawabi ga manema labarai a Abuja, shugaban kwamitin mika mulki, Boss Mustapha, ya jaddada cewa kararrakin da ke gaban kotu game da zaben kassar, ba zai hana gudanar da bikin mika mulki ba.

Ya ce, “Kwamitin na ci gaba da aiki kuma an kammala gyaran ofisoshi na shugaban kasa da mataimakin shugaban kasa.

Kayayyakin aiki da ke hukumomintsaro a shirye suke. An kuma tura jami'an tsaro na ma'aikatar harkokin wajen kasar da na 'yan sandan Najeriya zuwa ga zababben shugaban kasa da mataimakinsa.

“An kuma nada jami’ai na musamman ga zababben shugaban kasa da mataimakin shugaban kasa daga ma’aikatar harkokin waje da kuma hukumar leken asiri ta kasa.

“Tsarin mika mulki yana kan hanya, kuma ana yin duk kokarin da ake na ganin an daidaita koma. A ranar 29 ga watan Mayu, za a mika mulki ga sabon shugaban kasar cikin lumana, in ji Boss Mustapha.

Mustapha ya lura da cewa, an dora wa karamin kwamitin tsaro alhakin tabbatar da cewa babu wanda ya wasarere da aikin sa.

Ya ce, “Dukkanin kararraki, ko an warware ko ba a yi ba, ba za ta iya dakatar da aikin mika mulki ba. Shugaban kasa ba zai kara kwana daya a ofis ba. Kwamitin tsaro yana da alhakin tabbatar da cewa babu wani abin da ya faru da zai kawo cikas ga tsarin mika mulki. ’Yan Najeriya mutane ne masu bin doka da oda.

A wani bangare na mika mulki, Mustapha ya kuma ce sanya sunayen wasu mutane hudu da za su wakilci zababben shugaban kasa cikin tawagar gwamnatin tarayya a taron da bankin duniya ya sshirya.

Boss Mustapha ya kuma bayyana cewa zababben shugaban kasar ya zabi, Wale Edun da gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu, domin su kasance cikin kwamitin mika mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.