Isa ga babban shafi

IPOB ta umarci 'yan kabilar Igbo da ke Legas su koma gida

Kungiyar masu rajin kafa ‘yantacciyar kasar Biafara ta IPOB, ta sha alwashin daukar mataki mai tsauri kan ‘yan kabilar Yarabawan da suka ci zarafin kabilar Igbo a jihar Lagos da ke Najeriya.

Magoya bayan kungiyar IPOB kenan a Najeriya.
Magoya bayan kungiyar IPOB kenan a Najeriya. AFP PHOTO / PIUS UTOMI EKPEI
Talla

IPOB ta bayyana hakan n aa wata sanarwa da ta fitar ranar Alhamis, ta hannun sakataren yada labarai na kaasr, Emma Powerful.

Jaridar Dailytrust ta ruwaito cewa, matakin IPOB na zuwa ne, bayan rashin jutuwar da aka samu tsakanin ‘yan kabilar Yarabawa da kuma Igbo, bayan zaben shugaban kasar da aka yi a ranar 25 ga watan Fabrairu da kuma zaben gwamnonin da aka yi a ranar 18 ga watan Maris.

A cewar sanarwar, IPOB ta sha alwashin daukar matakin kan duk wani cin zarafi da aka yi wa ‘yan kabilar Igbo a jihar Lagos.

Kungiyar ta kuma gargadi ‘yan kabilar ta Igbo da su daina zuba jarin da ssuke yi a Legas din, tare da bukatar su da su koma yankunan su, inda IPOB ta kuma kara da cewa ya kamata ‘yan kabilar su fara kokarin kare kan su, ta hanyar kafa wata ‘yar karamar kungiya.

“Ra’ayin kyamar kabilar Igbo, barazana, hare-hare, da kuma yi wa ‘yan kasuwar Igbo sata, da barazanar da ake musu na su fice daga Legas, barazana ce ga daukacin kasar Biafra” in ji sanarwar.

“Abin takaici ne yadda shugabannin siyasa da na gargajiya na Yarabawa suka yi shuru kan yadda ake ci gaba da nuna kyama ga ‘yan kabilar Igbo a birnin Legas na Najeriya, wanda hakan ya nuna cewa suna kan hanya daya don fatattakar Ndigbo daga Legas.

“Muna kira ga Ndigbo maza da mata su shirya barin Legas. Mutumin da ba shi da wuri ne kawai zai ji haushi lokacin da wanda ya baka masauki ya ce ka bar gidansa.

A cewar kungiyar ta IPOB, ‘yan kabilar Igbo na da kasuwanni a duk sassan yankin kudancin Najeriya, wadanda suka isa daukar duk wadanda za su iya yin kaura daga Legas zuwa Kudu.

IPOB ta lura da cewa manyan kasuwannin da ke jihohin Ebonyi, Imo, Abia, Enugu, da Anambra sun isa su dauki dukkan ‘yan kasuwar da ke shirin komawa yankin.

“Ya kamata wadanda ke Legas su san cewa ba ta kowace hanya suke yin kasuwanci fiye da kasuwanci a yankin Kudu ba. Ya kamata su dawo don guje wa asarar rayukan su da dukiyoyinsu,” in ji IPOB.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.