Isa ga babban shafi
NAJERIYA-TSARO

Sojojin Najeriya sun kama wani jami'in ISWAP a Lagos

Ma’aikatar tsaron Najeriya ta sanar da kama wani da ake zargin ‘dan kungiyar Yan ta’addan ISWAP ne da ake zargin an tura shi Lagos domin aiwatar da manufar kungiyar.

Sojojin Najeriya dake sintiri a jihar Barno, ranar 12 ga watan Oktoba shekarar 20219.
Sojojin Najeriya dake sintiri a jihar Barno, ranar 12 ga watan Oktoba shekarar 20219. AFP/Archivos
Talla

Daraktan yada labaran ma’aikatar tsaron Janar Bernard Onyeuko yace an kama Ibrahim Musa, jami’in kungiyar lokacin da dakarun su suke samame a Sango Otta dake Jihar Ogun.

Onyeuko yace bayanan sirrin da suka samu yace Musa ya ziyarci Lagos ne domin sayen wasu kayayyaki da kungiyar ISWAP za tayi amfani da su a ayyukan ta a Maiduguri dake Jihar Barno.

Kakakin ma’aikatar tsaron yace dakarun su na ci gaba da gudanar da ayyukan su na sintiri akan bututun man kamfanin NNPC dake Gaun da Akute da Wawa 1 da Wawa 11 da Magbero domin dakile masu fasa su suna satar mai.

Janar Onyeuko ya kuma ce sun yi nasarar kama Oyeshola Saheed da ake zargi da fasa bututun man a Yankin Alimosho, kuma tuni ya bayyana wani Mr Akanbi a matsayin mai daukar nauyin aikin su a yankin.

Jaridar Daily Trust tace tuni dakarun suka karbe motoci da kayan aikin da masu fasa bututun man ke amfani da su domin gabatar da hukumomin da suka dace dan ganin an hukunta wadanda ake zargi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.