Isa ga babban shafi
Najeriya-Boko Haram

ISWAP ta tabbatar da mutuwar Shekau

Kungiyar mayaka masu ikirarin jihadi ta ISWAP da ke mubayi’a ga IS ta tabbatar da cewa tsohon shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau ya tarwatsa kansa da bam, ya mutu bayan da ya ki mika wuya a lokacin da suka yi masa kofar raggo a ranar 19 ga watan Mayu.

Abubakar Shekau, shugaban Boko Haram.
Abubakar Shekau, shugaban Boko Haram. AFP PHOTO / BOKO HARAM
Talla

 Hakan na kunshe ne a wani sakon murya na cikin gida da aka nada daga shugaban ISWAP din Abu Musab Albarnawi, wanda jaridar HumanAngle da ake wallafawa a intanet ta samu.

A jawabinsa, Albarnawi ya bayyana Shekau a matsayin jagoran rashin biyayya da rashawa, inda ya ce mayakansa ma sun yi farin ciki da mutuwarsa.

Ya ce cikin yanayi na wulaknci suka cimma Shekau, bayan da suka samu umurnin kama shi daga uwar kungiyarsu, wato ISIS, sakamakon yadda ya mayar da ran bil adama ba a bakin komai ba, inda yake kashe wadanda suka yi imani.

Albarnawi ya ce Shekau ya gwammaci wulakanci da azabar lahira a maimakon na duniya, shi ya sa ya kasha kansa, ya ki mika wuya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.