Isa ga babban shafi

An baza sojoji domin tabbatar da tsaro a Lagos

Yayin da a yau ake gudanar da zaben gwamnoni da ‘yan majalisu a sassan Najeriya, gwamnatin kasar ta baza sojoji a titunan birnin Lagos domin taimakawa wajen tabbatar da tsaro ga masu zabe. 

Wasu daga cikin sojojin da ke sintiri domin tabbatar da tsaro a birnin Lagos tun a ranar 1 ga watan Maris.
Wasu daga cikin sojojin da ke sintiri domin tabbatar da tsaro a birnin Lagos tun a ranar 1 ga watan Maris. AP - Sunday Alamba
Talla

Sabanin zaben shugaban kasar da aka yi ranar 25 ga watan jiya wanda ‘yan sanda da jami’an tsaron civil defence da kuma na farin kaya ne suka yi aikin samar da tsaro, a wannan karon anga sojoji cikin damara girke akan wasu manyan titunan birnin domin samar da tsaro. 

Wannan shi ne karo na farko da aka jibge sojoji akan titunan lagos lokacin zabe tun bayan zaben da aka yi a shekarar 2011. 

Wadannan sojoji sun kafa shinge inda suke binciken ababan hawa domin kama wadanda basu da izinin zirga-zirga, suna mika wa jami’an ‘yan sanda domin ganin sun fuskanci matakan shari’a. 

Bayanan da ke zuwa mana na nuna cewar sojojin sun datse hanyar Lagos zuwa Ibadan inda suka hana motocin da ke dauke da kaya motsawa. 

Jihar Lagos na daya daga cikin jihohin da zabensu ke dauke hankali musamman ganin yadda jam’iyyun adawa ke kokarin karbe iko daga gwamnatin da ke mulkin jihar. 

Ya zuwa lokacin rubuta wannan labari babu wani rahoton tashin hankalin da aka samu a birnin, yayin da jama’a ke ci gaba da fitowa suna kada kuri’un su. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.