Isa ga babban shafi

Zaben Najeriya: Ana cikin zulumi a jihar Legas

Wasu daga cikin mazauna birnin Lagos da ke kudancin Najeriya na cikin zullumi, inda suke fargabar yiwuwar samun tashin hankali a zaben gwamnan mai zuwa. 

Magoya bayan dan takarar jam'iyyar, Peter Obi kenan, yayin wani gangamin yakin neman zabe a Legas, ranar 11 ga Fabrairun 2023.
Magoya bayan dan takarar jam'iyyar, Peter Obi kenan, yayin wani gangamin yakin neman zabe a Legas, ranar 11 ga Fabrairun 2023. © Sunday Alamba/AP
Talla

Wannan na zuwa ne sakamakon yadda aka samu tashin hankali tsakanin Yarbawa da ‘Yan Kabilar Igbo, bayan Peter Obi ya doke Tinubu a jihar ta Lagos a zaben shugaban kasa. 

Bola Ahmed Tinu na jam'iyya mai mulki ta APC ne ya lashe zaben shugabancin kasar da yawan kuri'u, inda Atiku Abubakar na babbar jam'iyyar hamayya ta PDP ke biye, sai kuma Peter Obi daga jam'iyyar Labour da yazo na uku, inda Rabiu Musa Kwankwaso na jam'iyyar NNPP yazo na hudu.

Shiga alamar sauti domin sauraron rahoton da Abdulrahman Gambo Ahmad ya hada kan halin da ake ciki a jihar Legas din.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.