Isa ga babban shafi
Rahoto-INEC

INEC ta gana da hukumomin tsaron Najeriya don shirin tunkarar zaben Gwamnoni

Hukumar zabe a tarayyar Najeriya ta yi zama da dukkan masu ruwa da tsaki a harkar tsaro domin kintsawa zaben gwamnoni da ‘yan majalisun jihohi da za a gudanar a ranar asabar 18 ga watan nan na Maris.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu
Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu REUTERS - REUTERS TV
Talla

Zaben na Gwamnoni da ke shirin zuwa a karshen mako wanda zai gudana a jihohin kasar 28, akwai fargabar yiwuwar fuskantar rikici musamman lura da yadda al'ummar Najeriya suka fi mayar da hankali tare da sanya idanu kan zaben na Gwamna fiye da wanda ya gabace shi na shugaban kasa.

Wakilin mu na Abuja Mohammed Sani Abubakar ya hada mana rahoto dangane da shirin da INEC ta yi na tunkarar zaben Gwamnonin.

Ku latsa alamar sauti don sauraren rahoton. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.