Isa ga babban shafi

Hukumar INEC ta yi barazanar gurfanar da jam’iyyar PDP a gaban kotu

Hukumar Zaben Najeriya INEC ta yi barazanar gurfanar da babbar jam’iyyar adawa ta PDP a gaban kotu, bisa zargin bata sunan shugaban hukumar Farfesa Mahmoud Yakubu. 

Shugaban hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta INEC Farfesa Mahmood Yakubu.
Shugaban hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta INEC Farfesa Mahmood Yakubu. Premium Times Nigeria
Talla

Sakataren yada labaran hukumar Mr Rotimi Lawrence Oyekanmi ne ya bayyana wannan barzana a birnin tarayyar kasar Abuja. 

Shugaban hukumar shirya zaben Najeriya Farfesa Mahmud Yakubu
Shugaban hukumar shirya zaben Najeriya Farfesa Mahmud Yakubu © RFI Hausa

A cewar sa jam’iyyar PDP na yin duk mai yiwuwa wajen tabbatar da bata sunan shugaban hukumar ta hanyar zargin sa da magudi a zaben da ya gabata da kuma saura tsarin na’urar tantance masu zabe ta BVAS da gangan kawai don samun nasarar jam’iyyar APC.Ya ce bayan kiraye-kirayen sallamar shugaban hukumar da PDP ke yi, da kuma maka ta a kotyu bisa zargin hada kai da magudi, jam’iyyar na kuma ci gaba da bata sunan shugaban hukumar a idanun duniya da angiza ‘yan Najeriya kan su tsane shi ko ma kai masa hari. 

Alamun Jam'iyyar PDP da ta jagoranci Najeriya na shekaru 16
Alamun Jam'iyyar PDP da ta jagoranci Najeriya na shekaru 16 vanguardngr

Wannan ta sa a cewar sa donle ne hukumar ta dauki matakin shari’a a kan jam’iyyar. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.