Isa ga babban shafi

Na cika wa 'yan Najeriya dukkanin alkawuran da na dauka - Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari y ace ya cika wa ‘yan kasar dukkanin alkawuran da ya dauka a lokacin yakin neman zabe.

Shugaba Buhari kenan lokacin da yake karbar rantsuwar kama aiki a filin taro na Eagle Square da ke Abuja, ranar 29 ga Mayun 2019.
Shugaba Buhari kenan lokacin da yake karbar rantsuwar kama aiki a filin taro na Eagle Square da ke Abuja, ranar 29 ga Mayun 2019. Ng.gove.jpg
Talla

Mashawarcin shugaban na musamman kan al’amuran yada labarai Femi Adesina ne ya bayyana hakan, lokacin da yake gabatar da jawabi a wani taro da aka shirya a Damaturu da ke jihar Yobe.

Adesina ya kuma bayyana cewa babu wanda yake da hujjar da zai bata suna Buhari da sunan ya saci dukiyar kasa, domin kuwa bai azurta kansa da dukiyar gwamnati ba.

Shugaban ya kuma sha alwashin ci gaba da cika alkawuran da ya daukar wa Najeriya har zuwa lokacin da zai sauka daga mukamin shugabancin kasar.

Buhari ya yi ikirarin cewa ya cika wa ‘yan Najeriya alkawuran da ya daukar musu ranar 29 da watan Mayun 2015, ciki kuwa har da batun dakile ayyukan ta’addanci na mayakan boko Haram.

“A Arewa maso Gabashin Najeriya, Allah ya bamu ikon murkushe mayakan Boko Haram, tattalin arzikin kasa ya bunkasa, haka zalika mun samu galaba sosai wajen yakar rashawa a Najeriya,” in ji Buhari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.