Isa ga babban shafi

Zanga-zangar masu rajin kafa kasar Yarabawa a Legas ta haifar da asarar rai

Wani gangami da masu rajin kafa kasar Yarabawa suka gudanar a birnin Legas da ke najeriya, ya haifar da mutuwar mutum guda a yankin Ojota ranar Litinin.

Yadda masu rajin kafa kasar Yarabawa suka gudanar da zanga-zanga a birnin Legas.
Yadda masu rajin kafa kasar Yarabawa suka gudanar da zanga-zanga a birnin Legas. © vanguard
Talla

Kungiyar mai suna Yoruba Nation ta shirya gudanar da babban gangami a sassan na Legas, inda ta fara daga Ojota, yayin da take bukatar a kafa kasar Yarabawa daga Kudu maso Yammacin Najeriya.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Benjamin Hundeyin, ya shaidawa manema labarai cewa mutum da har yanzu ba a bayyana sunan sa ba, yam utu a yayin zanga-zangar.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da cewa tuni jami’an tsaro suka yi nasarar shawo kan lamarin, inda ta yi zargin cewa masu rajin kafa kasar Yarabawa na yunkurin tayar da zaune tsaye ne a jihar ta Legas.

Ya lura da cewa kungiyar ta Yoruba Nation bata sanar da hukumar ‘yan sanda game da gangamin nata ba.

A ranar uku ga watan Yulin 2021 ne, ‘yan sanda suka harbe wata yarinya mai suna Jumoke Oyeleke, lokacin da kungiyar rajin kafa kasar Yarabawa ke tsaka da gudanar da gangami.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.