Isa ga babban shafi

Najeriya: An yi garkuwa da fasinjojin jirgin ƙasa da dama a Edo

Rahotanni daga Najeriya na cewa wasu ‘yan bindiga sun yi awon gaba da fasinjoji da dama a wata tashar jirgin kasa da ke karamar hukumar Igueben a jihar Edo

Misali na 'yan bindiga a Najeriya
Misali na 'yan bindiga a Najeriya © Daily Trust
Talla

Wadanda abin ya shafa dai na dakon shiga jirgin kasa ne zuwa Warri da ke jihar Delta a lokacin da maharan suka far musu.

Kawo yanzu dai babu tabbas ko wani ya mutu a lamarin amma matafiyan da dama sun samu raunuka kamar yadda jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda a Edo, Chidi Nwabuzor, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Jami’in ya ce masu garkuwa da mutane dauke da bindigogi AK 47, sun mamaye tashar jirgin ne da yammacin ranar Asabar, inda suka rika harbi a iska kafin su yi awon gaba da matafiya da dama.

Wannan na zuwa ne kasa da shekara guda bayan da ‘yan ta’addan suka kaddamar da hari kan jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna inda suka kashe wasu fasinjojin jirgin tare da yin garkuwa da sama da 60 daga cikinsu.

Lamarin ya tilastawa gwamnatin tarayya dakatar da sufurin jirgin kasa a hanyar Abuja zuwa Kaduna sama da watanni shida kafin maido da shi baya-bayan nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.