Isa ga babban shafi

An kai hare-hare Ofisoshinmu sau 47 daga shekarar 2019 zuwa yanzu- INEC

Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya, INEC ta kira wani taron gaggawa da manyan jami’anta yau juma’a don tattaunawa kan yawaitar hare-hare kan Ofisoshinta a sassan kasar.

Shugaban hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta INEC, farfesa Mahmoud Yakubu.
Shugaban hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta INEC, farfesa Mahmoud Yakubu. © The Guardian Nigeria
Talla

Matakin kiran taron gaggawar na zuwa ne kwana guda bayan hari kan ofisoshin hukumar ta INEC a jihohin Ogun da Osun wanda ya kai ga kone tarin kayakin zabe ciki har da katunan zaben fiye da mutane dubu 60.

Hukumar ta ce abin takaici ne yadda aka farmaki ofisohinta har sau 47 daga watan Fabarirun 2019 zuwa yanzu, hare-haren da hukumar ta bayyana da wani yunkuri na hana jami’anta gudanar da ayyukansu a sassan Najeriyar.

Wata majiya daga hukumar ta INEC ta yi zargin cewa akwai masu kitsa makamantan hare-haren da gangan da nufin dakile kokarin jami’an hukumar na ganin an tabbatar da zabe mai sahihanci.

Rahotanni sun ce taron na INEC a yau juma’a zai tattauna matakan da ya kamata a dauka don bayar da kariya ga ofisoshin da kuma jami’an hukumar dai dai lokacin da zaben kasar ke ci gaba karatowa.

Yayin harin ‘yan daban na jiya alhamis kan ofishin INEC a Ogun, bayanai sun ce batagarin sun kone katunan zaben mutane dubu 65 da 699 baya ga wasu tarin kayaki masu muhimmanci na daban.

A watan Fabarairun sabuwar shekara ne dubban 'yan Najeriya ke shirin fita rumfunan zabe, don zaben shugaban kasa da 'yan majalisu da kuma gwamnoni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.