Isa ga babban shafi

Gwamnatin jihar Lagos ta kulle asibitoci 42 saboda rashin inganci

Gwamnatin Jihar Lagos ta sanar da kulle wasu asibitoci da cibiyoyin kula da lafiya 42 sakamakon binciken da ya gano ko dai rashin ingancinsu ko kuma an kafa su ba akan ka'ida ba.

Wani asibiti a jihar Lagos.
Wani asibiti a jihar Lagos. AFP
Talla

Shugabar hukumar kula da asibitoci ta jihar Lagos Abiola Idowu da ke sanar da wannan mataki yayin jawabinta kan ayyukan hukumar a watanni 9 da suka gabata, ta ce sun dauki wannan mataki ne don tabbatar da ganin al'umma na samun ingantacciyar kulawar lafiya.

Mrs Idowu ta ce cikin asibitoci dubu 1 da 40 da ta ziyarta daga watan Janairu zuwa Satumba ta rufe asibitoci 42, saboda abinda ta kira rashin bin ƙa'idodin da hukumar ta gindaya da suka kunshi rashin rajista da rashin kayan aiki ko kuma rashin kwararrun ma'aikatan jinya a wasun su baya ga laifin horar da dalibai ba bisa kaida ba.

A cewar shugabar, Jami'an hukumar sun mayar da hankali wajen duba dacewar cibiyoyin da tsaftarsu baya ga yanayin aikin da su ke yi, a wani yunkuri na tabbatar da cewa an tantance cibiyoyin kiwon lafiyar sau biyu a kowacce shekara kamar yadda doka ta tanada.

Shugabar hukumar kula da asibitocin ta jihar Lagos Mrs Abiola Idowu ta shawarci masu kafa asibitoci Daga karshe uwargida idowu ta shawarci masu asibitocin kansu da su fahimci dokokin gwamnati domin gudanar da ayyukan su da kuma kare lafiyar jama'a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.