Isa ga babban shafi

Wani gini ya nutse sakamakon ruwan sama a Lagos

Yanzu haka akwai mutane tara da suka makale  a cikin wani ginin bene da ake ci gaba da nutsewa cikin kasa a unguwar Maryland da ke birnin Lagos na Najeriya sakamakon ruwan saman da aka tafka kamar da bakin warya, lamarin da ya haddasa ambaliyar ruwa a sassan birnin.

Birnin Lagos a Najeriya na fuskantar ambaliyar ruwa duk shekara.
Birnin Lagos a Najeriya na fuskantar ambaliyar ruwa duk shekara. © guardian.ng
Talla

Hukumar Bada Agajin Gaggawa  ta Kasa NEMA ta  ce, ginin na nan a lamba 47,  layin Akinwunmi da ke rukunnin gidajen North Estate, Mende a unguwar ta Maryland da ke bababan  birnin Lagos, Ikeja.

Jami’in Hulda da Jama’a a Hukumar ta NEMA, Ibrahim Farinloye ya bayyana cewa, sun samu kiran waya da ke shaida musu halin da benen ke ciki na ci gaba da shigewa cikin karkashin  kasa, kuma har yanzu akwai mutane 9 da suka gaza fitowa daga ginin.

Rahotanni na cewa, mamallakin gidan, ya yi amfani da tsani domin tsira da ransa, amma Hukumar NEMA ta tuhume shi saboda yadda ya gaza tumtubar ta, inda daya daga cikin mutanen da suka makale ne ya yi karfin hali har ya kira wayar hukumar.

Dama dai Hukumar Hasashen Yanayi ta Najeriya ta yi gargadin cewa, za a samu ambaliyar ruwa a jihohjin Najeriya sakamakon ruwan saman da za a tafka a tsakan-kanin lokacin nan, yayin da tuni ambaliyar ta fara cinye gidaje kamar yadda aka yi zato.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.