Isa ga babban shafi

Kotu ta aike da wani basarake gidan yari na shekaru 15 saboda garkuwa da kansa

Babbar kotun jihar Lagos, ta yankewa basaraken Shangisha da ke karamar hukumar Alimosho, Michael Matiu Yusuf hukuncin shekaru 15 a gidan yari saboda samun sa da laifin yin garkuwa da kan sa.

Harabar babbar kotun Najeriya.
Harabar babbar kotun Najeriya. Premium Times Nigeria
Talla

Kotun dai ta yanke masa hukuncin ne tare da wani mai suna Adams Opeyemi Mohammed wanda ya taimaka masa wajen aikata damfarar, yayinda kuma aka sallami matar sa Abolanle.

Mai shari’a Hakeem Oshodi ya ce an yanke musu hukunci ne don ya zama izina ga wasu.

Tunda farko dai, mai gabatar da kara ya ce a ranar 5 ga watan Yulin shekarar 2017 ne, basaraken ya yi garkuwa da kansa da zummar haifar da rashin zaman lafiya, lamarin da ya ce ya sabawa sashe na 5 da ya haramta garkuwa da mutane na jihar Lagos a shekarar 2017.

Tuni dai gwamnatin jihar ta wancan lokacin karkashin Akinwunmi Ambode ta dakatar da basaraken daga matsayin sa, tun bayan da ‘yan sanda suka kama shi tare da Mohammed, kamar yadda sashe na 38 daya cikin baka na dokar masarautun jihar Lagos ta tanada. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.