Isa ga babban shafi
Najeriya - 'Yan bindiga

'Yan bindiga sun aika wasikar neman kudin fansa ga wani basarake a Sokoto

A Najeriya sakamkon katse layukan sadarwar wayoyin salalu a wasu yankunan jihar Sokoto, ‘yan bindigar yankin sun aike da rubutacciyar wasika ga dagacin Burkusuma dake karamar Hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto, inda suka bukace shi da ya hada musu kudin fansa daga iyalan mutanen da sukayi garkuwa da su.

Sojojin Najeriya yayin daukar horo.
Sojojin Najeriya yayin daukar horo. © Nigerian Defence Academy
Talla

A cikin wasikar da PREMIUM TIMES ta gani, 'yan fashin sun rubuta cikin harshen Hausa kuma sun ambaci sunayen wadanda ke hannunsu.

A baya -bayan nan mahara sun tsananta kai hare -hare kan kauyuka a kananan hukumomin Sabon Birni da Isa na jihar, inda suka kashe jami’an tsaro 21 a hare -haren da aka kai kauyukan Dama da Gangara.

Sun kuma kashe mutane 20 tare da yin garkuwa da wasu a ƙauyen Gatawa kwanan nan.

Sakamakon hare -haren da ake kai wa al'ummomin, dan majalisar mai wakiltar Sabon Birni ta Gabas a majalisar dokokin Sakkwato, Saidu Ibrahim, ya shaida wa PREMIUM TIMES kwanan nan cewa 'yan bindiga sun karbe ikon mazabarsa.

Isa da Sabon Birni na daga cikin kananan hukumomi 14 da aka katse hanyar sadarwar wayar salula don taimakawa ayyukan soji kan 'yan fashi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.