Isa ga babban shafi

Dodanni sun zane masu ibada a cikin Mujami'a

Wasu dodanni sun afka cikin wata Mujami’a a kauyen Shikal da ke karamar hukumar Langtang ta Kudu a jihar Filato da ke Najeriya, inda suka yi amfani da bulalai wajen tarwatsa wani taron masu ibada.

Wani dodo yayin bikin al'adu a Najeriya.
Wani dodo yayin bikin al'adu a Najeriya. © Massimo Rumi / Barcroft Images/Getty Images
Talla

Rahotanni sun ce doddannin da ake kira da ‘Masquerades’ a turance, sun isa harabar  cocin ne a yaayin da ake gudanar da addu’o’i, inda nan take suka afka wa taron mutanen da bulala.

Bayan lallasa masu badar ne kuma dodannin da suke rufe jikinsu da kayayyaki na al’adu, suka juya kan kayan kida na cocin suka kuma lalata su.

Kakakin ‘yan sandan jihar Filato , DSP Alfred Alabo  ya tabbatar da aukuwar lamarin, said ai bai yi karin bayani bayani ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.