Isa ga babban shafi

Rikicin kabilanci ya lakume rayukan mutane a Taraba

Ana faragabar mutuwar mutane da dama a Jihar Taraba dake Najeriya cikin su harda jami’an ‘Yan Sanda sakamakon wani rikicin kabilanci a kananan hukumomin Takum da Kurmi.

Wani hoto domin misali dake nuna 'yan bindiga.
Wani hoto domin misali dake nuna 'yan bindiga. Getty Images/iStockphoto - zabelin
Talla

Rahotanni daga rundunar ‘Yan Sandan Jihar sun ce jami’an su guda 3 aka kashe tare da kwace makaman su, bayan kashe kashen da aka samu na jama’a.

Bayanan dake zuwa mana na nuna cewar rikicin ya barke ne lokacin da jami’an tsaro suka bukaci dakatar da wani bikin al’adun gargajiya na kabilar Kutep dake Takum.

Wani mazaunin Takum, Bala John ya shaidawa Jaridar Daily Trust cewar daga bisani rikicin ya koma fada tsakanin Yan kabilar Kutep da Jukun, inda aka dinga jin harbe harben bindigogi.

Tuni hukumomin yankin suka kafa dokar hana fita domin dakile rikicin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.