Isa ga babban shafi

Mutane fiye da 20 sun kone kurmus a wani hadarin mota a jihar Oyo ta Najeriya

Akalla mutane 20 suka mutu a wani hadarin mota da ya faru da safiyar yau asabar a yankin kudu maso yammacin Najeriya, sakamakon taho mu gama da wata motar safa ta yi da wata karamar mota lamarin da ya kai ga konewar dukkanin motocin biyu.

Hadarin mota na haddasa asarar rayukan 'yan Najeriya fiye da dubu 5 kowacce shekara.
Hadarin mota na haddasa asarar rayukan 'yan Najeriya fiye da dubu 5 kowacce shekara. (Photo : Reuters)
Talla

Rundunar ‘yan sandan jihar Oyo da ke tabbatar da faruwar lamarin ta ce hadarin ya faru ne a daren jiya juma’a lokacin da motocin biyu makare da fasinja kowannensu ke tsala gudu dalilin da ya sanya suka yi taho mu gama tare da kamawa da wuta nan take.

Shugaban karamar hukumar Ibarapa, Gbenga Obalowo ya ce kirga gawarwakin mutane fiye da 20 a wadanda suka kone kurmus, ko da ya ke mutane biyu sun tsira da rayukansu wadanda tuni aka mika su ga asibiti don basu kulawar gaggawa.

Hadarin dai shi ne na baya-bayan nan da aka gani a jihar ta Oyo yankin da ake yawan samun asarar rayuka sakamakon taho mu gama tsakanin motocin Safa wadanda ke gudun wuce sa’a a kan tituna.

Rundunar ‘yan sandan dai ba ta bayar da cikakken bayan ikan hadarin ba, sai dai ta ce hadarin ya kashe mutane fiye da 20 tare da yin kira don ganin direbobi sun rage ganganci akan manyan tituna.

Hadarin mota tare da asarar dimbm rayuka akan tituna dai ba sabon abu ba ne a kan manyan hanyoyin Najeriya inda a ko a cikin watan Yuli makamancin wannan hadari akan hanyar Kaduna ya kashe mutane fiye da 30.

Wasu alkaluma sun nuna cewa a bara kadai, Najeriya ta yi asarar al’ummarta akalla mutum dubu 5 da 101 tare da jikkatar wasu fiye da dubu 30 a hadurran mota dubu 10 da 637 da hukumar kiyaye afkuwar hadurra ta tattara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.