Isa ga babban shafi

DSS ta musanta fitar da sanarwar gargadi kan harin ta'addanci a Abuja

Hukumar tsaron DSS ta yi watsi da wata sanarwa da ke kunshe da gargadi kan yiwuwar hare-haren ta’addanci a sassan Najeriya, sanarwa da ke ikirarin cewa jami’anta ne suka fitar wadda kuma tuni ta haddasa rudani bayan da ta karade shafukan sada zumunta a sassan kasar.

'Yan sandan Najeriya na hukumar tsaron farin kaya ta DSS.
'Yan sandan Najeriya na hukumar tsaron farin kaya ta DSS. AP - Sunday Alamba
Talla

Jaridar Vanguard da ake wallafawa a Najeriyar ta ruwaito kakakin hukumar ta DSS Dr Peter Afunanya cikin sanarwar da ya fitar a daren jiya litinin, ya ce sam sanarwar ta bogi kuma ba daga hukumarsu ta ke ba.

A cewar Afunanya hukumar ba ta fitar da wata sanarwar gargadi kan yiwuwar fuskantar harin ta’addanci a Abuja fadar gwamnatin kasar ko kuma kowanne sashe na Najeriyar ba.

Hukumar ta ce sanarwar bogin ta fito ne daga wasu masu neman tayar da zaune tsaye da ke shirin haddasa rudu da kuma tsoro a zukatan al’ummar kasar.

Sanarwar Bogin wadda ta yi ikirarin ta fito daga hukumar ta DSS ta bayyana yiwuwar fuskantar hare-hare a wasu yankuna na Abuja da suka kunshi Bwari da Gwagwalada da Kuje da kuma Abaji.

A baya-bayan nan hare-haren ta’addanci daga Boko Haram da kuma barazanar tsaro daga 'yan bindiga na ci gaba da tsannata a fadar gwamnatin ta Najeriya lamarin da ya sanya jama’a zaman dar-dar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.