Isa ga babban shafi

Najeriya: 'Yan ta'adda sun kai hari shingen binciken motoci a kusa da Abuja

Wasu sojoji da ba a tantance adadinsu ba sun mutu bayan da ‘yan ta’addan Boko Haram suka kai samame wani shingen binciken ababen hawa a kusa da dutsen Zuma Rock  da ke jihar Neja, kusa da babban birnin Tarayyar Najeriya, Abuja a daren Alhamis.

Hoton domin misali kan 'yan bindiga.
Hoton domin misali kan 'yan bindiga. © Depositphotos
Talla

Yankin da ke kusa da garin Madalla, ‘yan mitoci kadan daga garin Zuba da ke kan titin Abuja zuwa Kaduna.

Jaridar ‘Daily trust’ da ake wallafawa a Najeriya ta ruwaito cewa maharan sun isa wurin ne kusan karfe 7 na almuru, kuma suka bude wuta nan take.

Wata majiya ta ce ‘yan ta’addan sun karbe yankin na kusan mintuna 30, inda suka yi ta harbe harbe, bayan haka ne kuma suka dangana zuwa tintin abuja Kaduna.

mintuna 20 bayan da ‘yan ta’addan suka bar wurin ne sojoji daga barikin Zuma suka hanzarta zuwa wurin da lamarin ya auku, suka ci gaba da sanya ido a kan abubuwan da ke gudana a yanki.

Harin na zuwa ne a daidai lokacin da ake zaman tankiya a babban birnin Tarayyar Najeriya Abuja a kan yiwuwar harin ta’addanci.

Tun bayan da ‘yan ta’adda suka kai hari daidan yarin Kuje a Abuja, har ma suka kubutar da ‘yan uwansu  a ranar 5  ga watan Yuli al’ummar Abuja suke ta bayyana fargaba a kan lamarin tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.