Isa ga babban shafi

'Yan ta'adda na shirin kai hare-hare a jihohi 6 na Najeriya har da Abuja - NSCDC

A Najeriya, wasu kungiyoyin ta’addanci 2 na kitsa hare hare a kan yankunan arewa maso yammaci, tsakiyar kasar da kuma kudu maso yammacin Kasar, kamar yadda wata wasika da aka samu daga hukumar tsaron farin kaya ta Civil Defence ta nuna.

Taswirar Najeriya da ke nuna Abuja da Lagos.
Taswirar Najeriya da ke nuna Abuja da Lagos. AFP
Talla

Jaridar ‘Daily Trust’ da ake wallafawa a Najeriya ta ruwaito cewa hukumar Civil Defence ta aike wa da dukkannin rundunonin hukumar ta kasar ne wasikar, inda ta bayyna jihohin Lagos, Katsina, Zamfara, Kaduna da Kogi da kuma babban birnin tarayyar kasar, Abuja a matsayin inda ake shirin kai hare haren.

Mataimakin kwamandan rundunar Civil defence, D.D. Mungadi ne ya sanya wa takardar hannu.

A cikin wasikar, hukumar ta ce ta samu bayanai masu inganci da ke nuni da cewa kungiyar Boko Haram da ISWAP suna kintsa mayakansu, kuma sun sayo manyan makamai da suka hada da bindigogi masu saukar da jiragen sama da sauransu don kai hare hare a jihar katsina.

Sai dai da aka tuntube shi, kakakin rundunar Civil Defence, Shola Odumosu, ya ce takardar da aka samu ba daga gare su ta fito ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.