Isa ga babban shafi

Babu dan Boko Haram da ya rage a gidan yarin Kuje bayan harin 'yan bindiga

Ministan tsaron Najeriya Bashir Salihi Magashi, ya ce babu fursuna dan Boko Haram da ya rage a gidan yarin Kuje dake Abuja, bayan farmakin da gungun ‘yan bindiga suka kaiwa gidan gyaran halin a daren ranar Talata.

Allon babban gidan yari ko cibiyar gyaran hali dake Kuje a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya.
Allon babban gidan yari ko cibiyar gyaran hali dake Kuje a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya. © Daily Trust
Talla

Ministan ya bayyana haka ne a wata ganawa da yayi da manema labarai, yayin da ya kai ziyara gidan yarin na Kuje, inda yayi karin bayanin cewa, ‘yan bindigar sun kaddamar da farmakin ne da misalin karfe goma da rabi na daren Talatar, inda suka shiga cikin gidan gyaran halin ta karfin tsiya, tare da tseratar da fursunoni da dama, wadanda jami’ai ke kokarin gano su.

Magashi ya ce gidan yarin na daukar adadin fursunonin da yawansu ya kai 994, kuma alkaluma sun nuna cewar fiye da 600 daga cikinsu ne suka tsere a lokacin harin da ‘yan ta’addan suka kai, kuma akwai mayakan Boko Haram kimanin 60 zuwa 64 a cikinsu. Sai dai tuni aka sake kamo da dama daga cikin wadanda suka tsere daga gidan yarin.

Dangane da wadanda suka kaiwa gidan yarin na Kuje farmaki kuwa, ministan tsaron Najeriyar ya ce daga bayanan da suka tattara, suna kyautata zaton cewa mayakan Boko Haram ne maharan, kuma burinsu shi ne tseratar da ‘yan uwansu dake tsare.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.