Isa ga babban shafi

'Yan bindiga sun kai hari kan gidan yarin Kuje

Hukumar kula da gidajen yarin Najeriya ta tabbatar da cewa ‘yan bindiga sun kaiwa cibiyarta ta kula da gyaran hali dake karamar hukumar Kuje a Abuja, babban birnin tarayya.

Allon babban gidan yari ko cibiyar gyaran hali dake Kuje a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya.
Allon babban gidan yari ko cibiyar gyaran hali dake Kuje a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya. © Daily Trust
Talla

Cikin sanrwar da ya fitar da safiyar yau Laraba, mai magana da yawun hukumar Umar Abubakar, ya ce hadin gwiwar jami’ansu dake dauke da makamai tare da wasu jami’an tsaro sun samu nasarar tarwatsa maharan da suka kaddamar da farmakin.

Zuwa lokacin wallafa wannan labari dai babu karin bayani kan adadin mutanen da suka jikkata ko kuma suka rasa rayukansu yayin harin da aka kaiwa gidan yarin na Kuje dake Abuja.

Sai dai kakin hukumar kula da gidajen yarin Najeriya ya ce za su fitar da karin bayanai kan lamarin a nan gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.