Isa ga babban shafi

'Yan adawa sun bukaci tsige Buhari saboda matsalar tsaro

Takaddama ta kaure yau Laraba a Majalisar Dattawan Najeriya lokacin da aka bukaci tattauna matsalar tsaron da ta addabi kasar da kuma bukatar tsige shugaban kasar Muhammadu Buhaari saboda abin da 'yan majalisun suka kira gazawar sa wajen kare rayukan ‘yan kasar.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. Twitter/@BashirAhmad
Talla

Rahotanni sun ce shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawal yaki amincewa da bukatar tattauna tsige shugaban kasar, sai dai mahawara akan yadda matsalar tayi kamari da kuma baiwa shugaban kasar wa’adi domin shawo kan su, idan kuma ya gaza sai akai ga bukatar tsige shi.

Bayanai sun ce hana tattauna bukatar tsige shugaban kasar da Lawal yayi ta sanya wasu 'yan majalisar sama da 10 haure takalaman su domin ficewa daga zauren majalisar.

Kamar yadda rahotanni ke cewa, yunkurin janyo hankalin shugaban majalisar da shugaban marasa rinjaye Sanata Philip Aduda yayi, bayan sun kwashe sa’oi 2 suna tafka mahawara a asirce, yaci tura.

Yan Najeriya daga kowanne bangare sun fusata dangane da halin da kasar ke ciki saboda tabarbarewar tsaro, abinda ya kaiga salwantar da daruruwan rayuka da kuma asarar dukiyoyi.

Ko a makon jiya 'yan bindigar da suke garkuwa da mutane sun yi barazanar sace shugaban kasar Muhammadu Buhari da Gwamnan Kaduna Nasir El Rufai bayan sun fitar da faifan bidiyo inda suke lakadawa fasinjojin jirgin da suka kama duka.

A wannan mako, Yan bindigar sun kashe sojoji guda 3 a Abuja, babban birnin kasar da kuma kai hari kusa da kwalejin gwamnati dake Kwali, abinda ya tilasta rufe makarantar.

Bayan ficewar 'yan adawar, majalisar ta baiwa shugaba Buhari wa'adin makonni shida da ya magance matsalar tsaron, ko kuma ya fuskanci tsigewar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.