Najerya: Hukumar tsaron DSS ta bada rahotanni 44 gabanin harin Kuje -Wase
Mataimakin shugaban majalisar wakilan Najeriya Ahmed Idris Wase, ya bayyana cewa hukumar tsaron DSS ta gabatar da rahotanni a kan tsaro har guda 44 gabanin harin gidan yarin Kuje.
Wallafawa ranar:
A ranar 5 da watan Yuli ne ‘yan ta’adda suka kutsa gidan yarin Kuje da kje birnin Tarayyar Najeriya a Anuja, inda suka kubutr da sama da mutane 800 da ke daure a gidan, ciki har da ‘yan kungiyar Boko Haram da aka tsare.
Ya bayyana haka ne a yayin da yake tsokaci a kan kudirin da aka gabatar a majalisar a game da haramta amfani da Babura wajen sufuri a fadin kasar, wadda gwamnatin kasar take duba yiwuwar aiwatarwa.
Dan majalisa, Abubakar Makki Yelleman daga jihar Jigawa ne ya gabatar da kudirin a taron majalisar a yau Talata.
Wase ya ce lallai ya ga rahotani har 44 da hukumar tsaron DSS ta mika wa gwamnati a game da tsaro gabanin harin da ‘yan ta’adda suka kai gidan yarin Kuje.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu