Isa ga babban shafi

Jami'an tsaro sun yi bakin kokarinsu wajen kare gidan yarin Kuje - Minista

Ministan kula da harkokin ‘yan sandan Najeriya Mohammed Maigari Dingyadi ya ce jami’an tsaron dake kare gidan yarin Kuje a birnin Abuja sun yi iyakacin kokarinsu wajen dakile harin da ‘yan ta’adda suka kai, amma abin yafi karfinsu, saboda yawan maharan da kuma manyan makamansu.

Wasu motoci da mayakan ISWAP suka kone yayin farmakin da suka kaddamar kan gidan yarin Kuje dake birnin Abuja.
Wasu motoci da mayakan ISWAP suka kone yayin farmakin da suka kaddamar kan gidan yarin Kuje dake birnin Abuja. AP - Chinedu Asadu
Talla

Ministan ya bayyana haka a lokacin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai, jim kadan bayan kammala taron gaggawa na kwamitin tsaron Najeriya da shugaba Buhari ya jagoranta a fadar shugabancin kasar dake Abuja.

Dingyadi ya kuma bayyana cewa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya umarci hafsoshin tsaro da su tabbatar da daukar kwararan matakan da suka dace bayan gudanar da bincike kan musabbabin faruwar lamarin, domin hana maimaituwarsa.

Daya daga cikin motocin da 'yan ta'adda suka kone, yayin harin da suka kaiwa gidan yarin kuje a Najeriya.
Daya daga cikin motocin da 'yan ta'adda suka kone, yayin harin da suka kaiwa gidan yarin kuje a Najeriya. AP - Chinedu Asadu

Tuni dai kungiyar ISWAP wato tsagin da ya balle daga Boko Haram mai biyayya ga IS, ta dauki alhakin harin da gungun ‘yan bindiga suka kai gidan yarin Kuje da ke Abuja babban birnin Najeriya, wanda ya kai ga tserewar daruruwan masu laifi.

Wani faifan bidiyo da kungiyar ta fitar a ranar laraba mai dakika 38, ya nuna yadda mayakanta su ke shiga gidan yarin bayan fasa kofarsa da suka yi a daren ranar talata.

Yayin ziyarar da ya kai gidan yarin bayan harin da aka kai, Ministan tsaron Najeriya Bashir Salihi Magashi, ya ce babu fursuna dan Boko Haram da ya rage a tsare a gidan gyaran halin.

Magashi ya ce gidan yarin na daukar adadin fursunonin da yawansu ya kai 994, kuma alkaluma sun nuna cewar fiye da 600 daga cikinsu ne suka tsere a lokacin harin da ‘yan ta’addan suka kai, kuma akwai mayakan Boko Haram kimanin 64 a cikinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.