Isa ga babban shafi

Atiku ya kalubalanci Tinubu yin mahawarar sa’a guda

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya kuma ‘dan takarar Jam’iyyar PDP a zabe mai zuwa Atiku Abubakar  ya kalubalanci tsohon Gwamnan Lagos kuma ‘dan takarar APC, Bola Ahmed Tinubu domin su gudanar da mahawarar talabijin na sa’a guda domin tattauna batutuwan da suka shafi kasar.

Atiku da Tinubu
Atiku da Tinubu © Guardians
Talla

Yayin da yake mayar da martani akan matsayin kwamitin yakin neman zaben Tinubu cewar bai shirya mulkin Najeriya ba, saboda wasu batutuwa da yayi magana akai lokacin wata hirar da yayi a talabijin, Atiku ya bukaci Tinubu da amsa gayyatar gudanar da mahawara a tsakanin su ta sa’a guda.

Sanarwar da mai magana da yawun Atiku, Paul Ibe ya rabawa manema labarai tace, suna kalubalantar Tinubu da ya gabatar da kan sa domin gudanar da mahawarar awa guda da Tinubu domin nunawa duniya cewar yana da masaniya da kuma cikakkiyar lafiya kamar ‘dan takarar na su.

Ibe yace Atiku yayi mamakin kalaman da ’yan amshin shatar Tinubu suka yi dangane da hirar da yayi, musamman zargin cewar Atiku na gudanar da harkokin kasuwanci lokacin da yake aikin kwastam abinda ya sabawa doka.

Sanarwar ta kuma bayyana cewar Atiku ya mallaki shaidar kamala karatun digiri na biyu a Jami’ar Anglia Ruskin sabanin sauran ‘yan takarar zaben shugaban kasar da ake da shi yanzu, yayin da suka bukaci duk wani masi shaidar digiri irin wannan ko kasa da haka da ya gabatar domin jama’a su gani.

Ibe ya kuma ce jama’a na iya bincike domin tabbatar da sahihancin shaidar karatun sa, amma kuma hakan ba mai yiwuwa bane ga wasu ‘yan takara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.