Isa ga babban shafi

Kotu ta amince da shaidun da NDLEA ta gabatar kan zargin Abba Kyari

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta amince da bayar da dala 61,400 da mukaddashin kwamishinan ‘yan sandan da aka dakatar Abba Kyari ya bayar a matsayin cin hanci ga jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA.

Hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya NDLEA ta gurfanar da dakatatcen mukaddashin kwamishinan ‘yan sanda DCP Abba Kyari da wasu mutane shida bisa zargin safarar miyagun kwayoyi.
Hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya NDLEA ta gurfanar da dakatatcen mukaddashin kwamishinan ‘yan sanda DCP Abba Kyari da wasu mutane shida bisa zargin safarar miyagun kwayoyi. © Daily Trust
Talla

Mai shari’a Emeka Nwite a ranar Larabar da ta gabata ya aminci da wadannan kudade a matsayin hujja bayan hukumar NDLEA ta mika su ta hannun shaida na uku, Peter Joshua.

A ranar 22 ga watan Fabrairu ne aka gurfanar da Kyari tare da ACP Sunday Ubua da ASP Bawa James da Sifeto Simon Agirigba da John Nuhu, yayin da aka ce ASP John Umoru ya gudu.

Zaman Kotu

A zaman da aka ci gaba da sauraren karar, Joshua, wanda Sufeto ne  a hukumar yaki da fataucin muggan kwayoyi, wanda ke aiki da hukumar sa ido kan laifuka da leken asiri na hukumar ta NDLEA a Legas, ya shaida wa kotun cewa an mika masa kudin ne a ranar 25 ga watan Janairu bayan ya yi gwaje-gwaje na farko kan hodar iblis din.

Bidiyo

Hukumar ta NDLEA ta yi ikirarin cewa ta samu faifan bidiyo da ke nuna Kyari yana tattaunawa kan dala 61,400 a matsayin cin hanci da masu bincikenta domin hana gwajin kilogiram 17.55 na hodar iblis.

Wannan wani bangare ne na hodar iblis mai nauyin kilogiram 21.35 da masu laifin suka shigo da su cikin kasar a filin jirgin saman Akanu Ibiam dake Enugu a tsakanin ranakun 19 zuwa 25 ga watan Janairu.

Shaidan ya kuma bayar da wasu jakunan hodar ibilis guda 24 da aka kawo gaban kotun, da karin kwalin hodar ibilis guda uku, da kuma karin wasu 12 da aka daure daban-daban a cikin leda.

An dage sauraren karar har zuwa ranar 30 ga watan Agusta mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.