Isa ga babban shafi
Najeriya

Kotu ta amince NDLEA ta ci gaba da tsare Abba Kyari har sai ta kammala bincike

Wata Babbar kotu a Najeriya ta baiwa Hukumar yaki da safarar miyagun kwayoyi ta NDLEA umurnin ci gaba da tsare Mukaddashin kwamishinan ‘Yan Sandan Abba Kyari na karin kwanaki 14 domin gudanar da cikakken bincike akan tuhumar da ake masa na taimakawa masu safarar kwayoyi.

Abba Kyari jami'in dan sandan Najeriya da ke fuskantar tuhumar damfara da taimaka wa fataucin kwayoyi.
Abba Kyari jami'in dan sandan Najeriya da ke fuskantar tuhumar damfara da taimaka wa fataucin kwayoyi. © guardian.ng
Talla

Lauyan Hukumar NDLEA Mike Kassa ya bukaci kotun da ta basu karin lokaci domin kammala bincike dangane da tuhumar da ake yiwa mukaddashin kwamishinan ‘Yan Sandan saboda sarkakiyar dake tattare da aiki da kuma yiwuwar tafiya kasar waje domin tattara shaidu.

Mai shari’a Zainab Abubakar ta amince da bukatar Hukumar domin bata lokacin gudanar da bincike akan zargin.

Bani da lafiya - Abba Kyari

Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sandan Abba Kyari ya shigar da kara kotu inda yake bukatar ta bashi damar amfani da dokokin kasa wajen kare hakkokin san a Bil Adama wajen sakin sa daga inda ake tsare da shi saboda dalilan rashin lafiya da suka hada da cutar suga da hawan jini, amma mai shari’ar ta dage sauraron karar zuwa ranar alhamis mai zuwa.

A makon jiya ne Rundunar Yan Sandan Najeriya ta kama Abba Kyari ta kuma mikawa Hukumar NDLEA wadda tayi shelar neman sa ruwa a jallo, bayan yaki amsa gayyata domin bada ba’asi dangane da zargin da ake masa na alaka da masu safarar kwayoyi.

Bidiyon zargin Abba Kyari

NDLEA ta gabatar da wani faifan bidiyo dake nuna Kyari na tattaunawa da wani jami’in ta akan yadda zasu raba wata hotar ibilis da aka kama a tashar jiragen Enugu bayan an shiga da ita kasar daga Habasha.

Wannan kamu ya haifar da cece kuce a ciki da wajen kasar saboda danganta shi da Kyari wanda ake gani a matsayin daya daga cikin jaruman rundunar Yan Sandan Najeriya dake yaki da masu aikata manyan laifuffuka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.