Isa ga babban shafi
Najeriya - Abba Kyari

Abba Kyari ya musanta zargin da NDLEA ke masa a gaban kotu

Hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya NDLEA ta gurfanar da dakatatcen mukaddashin kwamishinan ‘yan sanda DCP Abba Kyari da wasu mutane shida bisa zargin safarar miyagun kwayoyi.

Hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya NDLEA ta gurfanar da dakatatcen mukaddashin kwamishinan ‘yan sanda DCP Abba Kyari da wasu mutane shida bisa zargin safarar miyagun kwayoyi.
Hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya NDLEA ta gurfanar da dakatatcen mukaddashin kwamishinan ‘yan sanda DCP Abba Kyari da wasu mutane shida bisa zargin safarar miyagun kwayoyi. © Daily Trust
Talla

Wadanda ake tuhumar tare da Kyari sun hada da ACP Sunday Ubua, ASP Bawa James, Insfekta Simon Agirigba, John Nuhu, sai kuma ASP John Umoru wanda aka ce ya tsare.

Sauran sun hada da Chibunna Patrick Umeibe da Emeka Alphonsus Ezenwanne.

Kyari ya ki amsa laifin da ake tuhumarsa

Lokacin da aka karanta wa wadanda ake tuhuma tuhume-tuhume takwas, biyu daga cikin wadanda ake tuhumar, Umeibe da Ezenwanne sun amsa laifin da ake tuhumar su da su, amma Kyari da sauran jami’an sun musanta aikata laifin.

Faifan bidiyo

Hukumar NDLEA ta ayyana neman Kyari ne bayan da ta samu faifan bidiyo da ke nuna yadda ya ke tattaunawa da masu bincikenta kan cinikin kwayoyi.

An kama sauran wadanda ake tuhumar ne a ranar 19 ga watan Janairu a filin jirgin sama na Akanu Ibiam, dake Enugu, inda suka amsa cewa su ne masu jigilar kwayoyi.

A cikin tuhume-tuhumen, Abba Kyari, ACP Sunday Ubua, ASP Bawa James, Insifeto Simon Agirigba, da Insifekta John Nuhu, an ce dukkansu jami’an hukumar leken asiri ta Intelligence Response Team (IRT) sun yi cinikin hodar iblis mai nauyin kilogiram 17.55 tsakanin ranar 19 zuwa 25 ga watan Janairu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.