Isa ga babban shafi

Najeriya: Gwamnatin Zamfara ta dakatar da sarkin da ya ba dan bidiga sarauta

Gwamnan jihar Zamfara a Najeriya Bello Matawalle ya dakatar da Sarkin Birnin ‘Yan doton Tsafe a karamar hukumar Tsafe, Alhaji Aliyu Marafa, sakamakon sarautar da ya bai wa wani kasurgumin dan bindiga,  Ado Alero.

Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle
Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle premiumtimesng
Talla

Wasu majiyoyi sun ce an yanke shawarar nada wa dan bindiga sarautar ce duba da irin gudummawar da ya bayar a wajen lalubo zaman lafiya kwanan nan a tsakanin masarautar ‘Yandoto da ‘yan bindigan da ke addabar yankunan karamar hukuma Tsafe.

Sai dai a cikin wata sanarwa, sakataren gwamnatin jihar,  Kabiru Balarabe Sardauna, ya ce gwamnatin Zamfara ta nesanta kanta daga wannan al’amari da ya gudana a ‘Yandoto, inda ya sanar da dakatar da sarkin da ya yi nadin nan take.

Gwamnatin ta kuma kaddamar da wani kwamiti mai mutane 6 a karkashin jagorancin Yahaya Chado Gora don gudanar da bincike a kan abin da ya kai ga wannan mataki da sarkin ya dauka.

Sai dai wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa  wasu jami'an gwamnati sun halarci bikin nadin da aka wa Ado Aleru, haka zalika sun ga dimbim 'yan bindiga bisa babura suna cahsewa a wajen bikin nadin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.