Isa ga babban shafi

Ba zan huta ba sai na lalubo wa ‘yan Najeriya sauki - Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhariya tabbatar wa da ‘yan Najeriya cewa ba zai hut aba har sai ya kawo musu sauki a kan matsalolin da ke damun su da suka hada da tsaro da tsadar rayuwa.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. AP - Julien de Rosa
Talla

Shugaban ya bada wannan tabbacin ne a sakonsa na Sallah ga al’ummar Musulmi da sauran ‘yan kasa.

A wata sanarwa da mai taimaka masa a harkar yada labarai, Malam Garba Shehu ya raba, Buhari ya ce yana sane da halin  kunci da al’ummar kasar ke ciki, kuma yana aiki tukuru don warware su.

Shugaba Buhari ya bayyana fatan cewa wannan lokaci na Sallah babba zai kasance silar samun albarka da zaman lafiya da ci gaban ‘yan Najeriya, yana mai bayyana ykinin cewa zamantakewa da kwanciyar hankali za su inganta a kasar.

Shugaban ya shawarci Musulmai da su yi riko da koyarwar addininsu don  ganin daidai a al’amuransu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.