Isa ga babban shafi

Babu ruwana da tazarce - Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya shaida a Firaministan Birtaniya Boris Johnson cewar bai taba tunanin neman wa’adi na 3 na mulki ba, saboda haka a shirye ya ke ya mika mulki da zarar wa’adin sa ya kare a shekara mai zuwa.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da Fira ministan Birtaniya Boris Johnson.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da Fira ministan Birtaniya Boris Johnson. © Nigerian presidency
Talla

Yayin ganawa da Firaministan Birtaniya Boris Johnson a Kigali dake kasar Rwanda wajen taron shugabannin kasashen renon Ingila ko kuma Commonwealth, Buhari ya ce  yace shima wanda yayi kokarin yin tazarcen wajen neman wa’adi na 3 a cikin kasar bai wanye lafiya ba.

Sanarwar da mai bai wa shugaban shawara a kan harkokin yada labarai Femi Adeshina ya raba wa manema labarai, ta ce yayin ganawar Johnson ya tambayi Buhari ko zai tsaya takara domin neman wa’adi na 3, amma nan take Buhari ya ce 'a’a, domin wanda ya gwada yin haka a Najeriya bai wanye lafiya ba'.

A ranar 29 ga watan Mayun shekara mai zuwa ake saran shugaba Buhari ya mika mulki ga zababben shugaban kasar da ‘yan Najeriya za su zaba domin maye gurbinsa, bayan kammala wa’adin sa na biyu.

 

Dangane da shugaban 'yan awaren IPOB Nanmdi Kanu dake tsare kuwa da ake zargin an hana lauyoyin sa ganawa da shi, Buhari ya ce babu gaskiya cikin lamarin domin kotu ce ke rike da shi domin amsa tambayoyi a kan irin kalaman batancin da ya dinga yi a kan Najeriya daga Birtaniya.

Buhari ya shaida wa Johnson cewar, Kanu ya samu mafaka a Birtaniya inda ya dinga bata sunan Najeriya kafin jami’an tsaro su cafko shi lokacin da ya bar kasar, kuma yanzu haka yana gaban kotu.

Shugaban ya ce Kanu na da hurumin kare kansa, kuma lauyoyin sa na ganawa da shi, yayin da ya shaida wa Johnson cewar kar ya manta fa, an taba bada shi beli amma ya gudu, saboda haka yanzu a kan wane hurumi za’a sake bada shi?

Dangane da matsalar tsaron Najeriya kuwa, Buhari ya shaida wa Firaministan cewar suyi kokarin tabbatar da zaman lafiyar Libya, domin ta haka ne Najeriya da makotanta zasu zauna lafiya, ganin yadda kawar da Muammar Ghadafi daga karagar mulki ya sa masu tsaronsa suka bazama da makamai yankin Sahel suna aikata laifuffuka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.