Isa ga babban shafi

Gwamnati ta na kokarin kawo karshen ayyukan ta'addanci - Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewar gwamnatin sa na iya bakin kokarin ta wajen ganin ta kawo karshen ayyukan ta’addancin da suka addabi kasar domin ganin an gudanar da zabe mai zuwa cikin kwanciyar hankali.

Shugaban Najeriya Muhammdu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammdu Buhari © lailasnews
Talla

Buhari yace babu tantama za’a yi nasarar murkushe ‘Yan ta’adda da mutanen da basa bukatar ganin Najeriya ta zauna lafiya muddin jama’ar kasar suka hada kan su.

Bukin 'June 12'

Shugaban dake jawabi ga ‘Yan Najeriya kan bikin ranar dimokiradiya ta ‘June 12’,  yace kullum a cikin tashin hankali yake dangane da yan uwa da iyalan wadanda suka fuskanci ayyukan ta’addanci ko kuma akayi garkuwa da su.

Buhari yace shi da hukumomin tsaron kasar na iya bakin kokarin su wajen ganin sun kubutar da yan kasar maza da mata suka samu kan su a cikin irin wannan mummunar tashin hankali.

Ga wadanda suka rasa rayukan su ta irin wannan hanya kuwa, shugaban yace zasu ci gaba da kokarin ganin an yiwa iyalan su adalci akan wadanda suka aikata laiffukan, yayin da ya sha alwashin kubutar da wadanda ake garkuwa da su da kuma hukunta masu garkuwa da mutanen.

Garambawul ga bangarorin tsaro

Shugaban yace sun yiwa wasu daga cikin bangarorin tsaron kasar garambawul, kuma wasu daga cikin kayan tsaron da suka sayo shekaru 3 da suka gabata sun iso kuma an fara amfani da su yanzu haka domin murkushe irin wadannan mutane.

Buhari yace muddin ‘yan Najeriya suka hada kan su babu abinda zai hana su samun nasara akan wadannan ‘yan ta’adda.

Tsaftacacen zabe

A bangare daya shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewar wanda zai gaje shi zai fito ne ta hanyar tsaftacacen zabe wanda duniya zata amince da shi.

Yayin da yake jawabi ga al’ummar kasar saboda zagayor ranar bikin dimokiradiya ta ‘June 12’, shugaban yayi alkawarin gudanar da karbaben zabe, cikin kwanciyar hankali wanda kowa zai amince da sahihancin sa.

Hada hannu

Buhari ya bukaci masu ruwa da tsaki a fuskar dimokiradiya da su hada hannu wajen ganin an tafiyar da shirin mika mulki ga sabuwar gwamnati mai zuwa cikin lumana, yayin da ya bayyana yakinin sa na ganin haka ya samu saboda abinda ya kira alamomin da ya gani.

Shugaban ya yaba da irin matakan da jam’iyyun siyasar kasar suka  dauka na gudanar da zaben fidda gwani domin tsayar da ‘yan takarar zabe mai zuwa, yayin da ya bukace su da cigaba da bin wannan tsarin har zuwa lokacin zaben kasa baki daya.

Gargadi

Buhari yayi jan kunne ga masu kallon zaben a irin yanayin ko-a-mutu-ko-ayi-rai, inda ya shaida musu cewar dimokiradiya na tafiya ne akan tafarkin jama’ar da suka fi yawa, kuma dole ne a samu wanda ya samu nasara da wanda ya samu akasi.

Shugaban ya kuma bukaci ‘yan takarar da su mayar da hankali akan gabatar da manufofin su da zasu janyo hankalin jama’a maimakon batawa abokan hammaya suna ko kuma tinzira jama’a dan gudanar da tashin hankali.

'Yan takara

Buhari ya shaidawa ‘yan takarar cewar a matsayin su na shugabanni ya zama wajibi su nunawa duniya jagoranci na gari domin kuwa ana kallon su daga ko ina, kamar yadda kasashen Afirka ke kallon Najeriya ta gabatar da jagoranci na gari.

Masu kada kuri'u

Ga masu kada kuri’a kuwa, shugaban ya shaidawa musu cewar gwamnatin sa a cikin shekaru 7 da suka gabata, ta zuba jari a matakai daban daban domin inganta harkokin zabe da yadda ake gudanar da shi domin kare kuri’un jama’a da kuma tabbatar da sun yi tasiri a kowanne mataki.

Buhari ya bayyana cewar bangarorin gwamnati guda 3 da suka hada da zartarwa da majalisa da kuma shari’a na tsaye wajen aiki tare domin aiwatar da wadannan shirye shirye a zabe mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.