Isa ga babban shafi

'Yan bindiga sun nemi miliyoyin naira kafin sakin wadanda suka sace a Zamfara

Rahotanni daga yankin arewa maso yammacin Najeriya sun ce, ‘yan ta’adda ko kuma ‘yan bindiga sun nemi a biyasu makudan kuddaden da yawansu ya kai akalla naira miliyan 145, kafin su saki mutane kusan 30 da suka yi garkuwa da su a jihar Zamfara.

Yan bindiga a Najeriya
Yan bindiga a Najeriya © Daily Trust
Talla

Kafar talabijin na Channels dake Najeriya ya ruwaito sakataren kungiyar wadanda abin ya shafa na jihar Zamfara Ashiru Zurmi, na cewa ‘yan bindigar na tuntubar kungiyar tasu, ta hanyar amfani da daya daga cikin wayoyin wadanda suka yi garkuwa da su, inda suka bukaci da a biyasu makudan kudaden da suka nema a matsayin kudin fansa.

Idan za a iya tunawa dai, a ranar Asabar da ta gabata, ‘yan bindiga suka sace mutane fiye da 50 a yankin Dogon Awo dake tsakanin Bakura da Tureta a kusa da iyakar Sokoto.

Bayanai sun ce gwamman mutanen da ‘yan ta’addan suka sace na kan hanyar komawa gidajensu dake Zamfara ne daga wani bikin aure da suka halarta a jihar Sokoto.

Sai dai jin kadan bayan fadawa hannun maharan wasu daga cikin matafiyan da adadinsu ya zarce 20 suka samu nasarar tserewa, inda bayanai suka ce jami’an tsaro ne da kuma ‘yan Bijilan suka ceto wasunsu.

Zamfara na daga cikin jihohin arewacin Najeriya masu fama da matsalar tsaron ta’addancin ‘yan bindiga masu kisa, garkuwa da mutane da kuma sace dimbin dukiyar jama’a, matsalar da tilastawa dubban mutane yin gudun hijira daga kauyukansu zuwa cikin birane, yayin da wasu ma ke tsallakawa cikin Jamhuriyar Nijar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.