Isa ga babban shafi

IMF ta gargadi Najeriya kan karuwar basuka da kuma raguwar kudaden shigarta

Hukumar bada lamuni ta Duniya IMF ta gargadi Najeriya kan yadda kudaden shigar kasar ke raguwa da kuma basukan da take ci, inda bayyana cewar daga shekarar 2026 kasar za ta koma amfani da kudaden harajin da ta ke tarawa wajen biyan kudin ruwan bashin da ta ciwo.

Tambarin asusun bada lamuni na Duniya IMF.
Tambarin asusun bada lamuni na Duniya IMF. REUTERS - Yuri Gripas
Talla

Jami’in Hukumar a Najeriya Ari Asien ya kuma bayyana cewar ganin yadda gwamnatin kasar ke kashe naira biliyan 500 kowanne wata a matsayin tallafin man fetur, tallafin na iya kaiwa naira triliyan 6 a karshen wannan shekara.

IMF ta bukaci kawo karshen biyan kudaden tallafin da kuma taka tsan tsan wajen rance da ake ciwo wa, domin sake dabarun ci gaban kasar da kuma dakile hauhawan farashin kayayyaki tare da bangaren musayar kudaden waje.

Hukumar ta ce irin arzikin da Allah Ya wadata kasar da shin a sabbin hanyoyin samun makamashi da tarin ma’adinan dake karkashin kasa da dabarun kirkiro ayyukan yin a da matukar tasiri wajen karkata hanyoyin ci gaban kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.