Isa ga babban shafi
Najeriya - IMF

IMF ya bukaci Najeriya ta soke tallafin mai da farashin canjin kudi na hukuma

Asusun ba da lamuni na duniya IMF ya sake yin kira ga gwamnatin Najeriya da ta soke tallafin man fetur da kuma farashin canjin kudade na hukuma, tare da daukar matakan rage radadin da hakan zai haifarwa marasa karfi.

Shugabar asusun ba da lamuni na duniya IMF, Kristalina Georgieva.
Shugabar asusun ba da lamuni na duniya IMF, Kristalina Georgieva. Daniel LEAL AFP/File
Talla

Kiran na IMF ya zo ne bayan da a ranar 24 ga watan Janairun da ya gabata, gwamnatin Najeriya ta bayyana dakatar da shirinta na cire tallafin man fetur a bana, matakin da asusun ya ce ba zai dore ba.

Wannan ba shi ne karo na farko da asusun IMF ke kira ga gwamnatin Najeriya kan bukatar cire tallafin mai kwata kwata ba, inda a baya bayan nan asusun ba da lamunin na duniya ya kara da bukatar soke da tsarin banbanta matakin canjin kudade na hukuma karkashin bankin CBN da kuma na bayan fage, ma’ana gwamnati ta kyale kasuwa ta fayyace darajar Nera.

Sai dai a yayin zantawar sa da sashin Hausa na RFI, Dr Kasim Garba Kurfi masanin tattalin arziki a Najeriya, ya ce bai yi mamakin kiran da IMF ya sake yi wa Najeriya ba, la’akari da cewar dole hakan ta faru ga kowace kasa da karbar bashi ya zamewa dole la’akari karin maganar da ke cewa ‘duk wanda ya ci ladan kuturu dole ya yi masa aski’

A bangaren bukatar maida kasuwar canjin kudaden kasashen ketare zuwa ta bai daya kuwa, Dr Kurfi ya ce matakin zai taimaka wajen kawo karshen karancin Dala a Najeriya, sai dai illar kuma da ke tattare da hakan itace dimbin bashin biliyoyin dalolin da ke kan kasar zai kusan ninka, da zarar an fara aiwatar da bukatar asusun lamunin na duniya.

00:57

Dr Kasim Garba Kurfi akan kiran da IMF ya yiwa Najeriya kan soke tallafin mai

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.