Isa ga babban shafi
Najeriya-IMF

IMF ta bukaci Najeriya ta janye tallafin mai da wutar lantarki

Asusun bada lamuni na duniya ya yi kira ga gwamnatin Tarayyar Najeriya da ta janye gaba daya tallafin da take bayarwa na mai da wutar lantarki.

Tambarin Asusun Bada Lamuni na Duniya.
Tambarin Asusun Bada Lamuni na Duniya. REUTERS - Yuri Gripas
Talla

bayan wata ziyara da jami’ansa suka kai Najeriya, asusun ya kuma yi kira ga hukumomin kasar su karya darajar kudin kasar da tare da rage kudaden gudanar da gwamnati don dakile rashin ci gaba da ake samu a kasar.

A wata sanarwa, asusun ya  bukaci gwamnatin ta dauki batun janye tallafin mai da wutar lantarki  marasa amfani a shirinta na shekara mai zuwa da mahimmanci.

Sai dai ya yi kira ga hukumomin su lalubo hanyoyin saukaka wa aal’umma radadin da janye tallafin zai taho da shi.

Asusun ya kuma lura cewa tattalin arzikin Najeriya na farfadowa daga masassara sakamakon manufofin gwamnati da kuma tashin farashin danyen mai a kasuwannin duniya, inda ya kara da cewa kasar ya fita daga matsalar tattalin arziki da ta fada ciki da wuri fiye da yadda aka zata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.