An dakatar da limamin Masallacin Juma'a na Apo saboda sukar gwamnati
Kwamitin kula da babban masallacin Juma’a na Apo Kwatas dake birnin Abuja a Najeriya, ya dakatar da limamin Masallacin Shiekh Nura Khalid sakamakon kalaman da ya furta yayin gabatar da hudubar Sallar Juma'ar da ta gabata.
Wallafawa ranar:
Yayin jawabin da ya gabatar, malamin ya bukaci jama’a da kada su fita zabe har sai cimma yarjejeniya tsakanin mutane da ‘yan siyasa kan kare hakkokinsu.
Malamin ya kuma caccaki gwamnati kan gazawar ta wajen magance matsalolin tsaron da suka addabi ‘yan Najeriya.
Sai dai a cikin wata sanarwa shugaban kwamitin kula da Masallacin na APO, kuma tsohon Sanata Sa’idu Muhammad Dansadau ya ce kamata yayi malamin ya shawarci mutane da su ki zabar baragurbin ‘yan siyasa zuwa kan mukamai, amma ba ya furta kalaman tunzura su kin fita zaben ba.
Shiekh Nura Khalid dai yayi fice wajen jan hankalin hukumomi a Najeriya a duk lokacin da yake ganin an aikata ba daidai ba, inda a lokuta da dama ya ke amfani da kakkausan harshe wajen sukar da ya kan yi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu