Isa ga babban shafi
Najeriya-'Yan bindiga

'Yan bindiga sun sace mutane 11 a wani kauyen Katsina bayan janye sojoji

A Najeriya, biyo bayan janyewar da sojoji suka yi a kauyen Shimfida na karamar hukumar Jibia a jihar Katsina, ‘yan bindiga sun shiga kauyen a daren Juma’a, inda suka yi awon gaba da  mutane 11.

'Yan bindiga na ci gaba da addabar mutane a yankin arewacin Najeriya.
'Yan bindiga na ci gaba da addabar mutane a yankin arewacin Najeriya. The Guardian Nigeria
Talla

Tun da farko sashen Hausa na RFI ya  kawo rahoton yadda mutane 7 suka mutu a sakamakon wani turmitsitsi da ya auku  a lokacin da dimbim jama’a ke barin kauyen sakamakon janye sojoji da hukumomin kasar suka yi.

A makarantar sakanadiren gwamnati ta Shimfida, mai nisan kilomita 27 daga garin Jibia  ne da ma  aka girke sojojin da aka janye a ranar Alhamis da ta gabata.

Shimfida na daya daga cikin yankunan da ayyukan ‘yan bindiga, masu satar mutane da yi wa mata fyade suka yi wa mummunar illa a jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.