Isa ga babban shafi
NAJERIYA-TSARO

Najeriya ta samu 'Yan gudun hijira miliyan guda a shekara guda

Hukumar Kula da ‘Yan gudun hijira da kuma mutanen da suka rasa matsugunin su a Najeriya tace ‘Yan kasar sama da miliyan guda suka rasa matsugunan su a cikin shekara guda sakamakon tashe tashen hankula.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari © Nigeria presidency
Talla

Kwamishiniyar dake kula da Hukumar Imaan Suleiman Ibrahim ta bayyana haka inda take cewa ya zuwa wannan lokacin mutanen da suka rasa matsugunan su a fadin kasar sun kai miliyan 3.

Shugabar hukumar tace Najeriya zata karbi ‘Yan gudun hijira 73,000 daga kasashe 23 a shekara mai zuwa, yayin da zata kwaso ‘Yan Najeriya 500,000 da suka makale a kasashen Libya da Chadi da Nijar da Kamaru da kuma Mali.

Imaan Ibrahim tace hukumar ta na shirin gina matsugunan ‘Yan gudun hijira a Jihohin Borno da Kano da Edo da kuma Katsina, yayin da aka cire Zamfara saboda matsalar da aka samu wajen samun fili.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.