Isa ga babban shafi
Najeriya

Adadin wadanda suka mutu a ruftawar ginin Ikoyi ya kai 40

Adadin wadanda da suka mutu sakamakon rubzawar da gini mai hawa 21 yayi kansu a unguwar Ikoyi dake birnin Legas ya karu zuwa mutane 40.

Gini mai hawa 21 da ya rushe a unguwar Ikoyi dake jihar Legas a Najeriya.
Gini mai hawa 21 da ya rushe a unguwar Ikoyi dake jihar Legas a Najeriya. PIUS UTOMI EKPEI AFP
Talla

A ranar Alhamis ne dai jami'an ceto dake kokarin ciro mutanen da suka makale a karakashin dogon ginin da ya rushe suka tabbatar da mutuwar Femi Osibona, shugaban Kamfanin 'Fourscore Homes Limited', wanda ya rasu sakamakon rutsawar hatsarin yayi da shi.

Osibona dai shi ne mamallakin kamfanin da ya gina benen mai hawa 21 da ya ruguje a ranar Litinin, 1 ga watan Nuwamba.

Akwai dai fargabar cewa akalla mutane 70 zuwa 100 ko sama da hakan ke cikin ginin da ya ruguje.

Tuni dai gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu, ya sanar da kafa wani kwamitin kwararru mai manbobi 5 da za su gudanar da bincike dangane da rugujewar da dogon ginin yayi a unguwar Ikoyi.

Sanwo-Olu ya ce kwamitin binciken zai shafe kimanin wata guda domin kammala aikinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.