Yawan mutanen suka mutu sakamakon rushewar dogon bene a Legas ya kai 38
Hukumomi a jihar Legas dake Najeriya sun ce adadin wadanda suka mutu sakamakon rugujewar wani bene mai hawa 21 a unguwar Ikoyi ya kai 38, a yayin da aka fara yanke kauna ga samun wadanda ke da sauran numfashi.
Wallafawa ranar:
Michael Kuduson da ya ziyarci wurin ya hada mana rahoto a kai.
Halin da ake ciki dangane da aikin ceto mutanen da gini mai hawa 21 ya rubzawa a Legas
A Alhamis din nan ne dai jami'an ceto dake kokarin ciro mutanen da suka makale a karakashin ginin mai hawa 21 da ya rushe a Legas suka tabbatar da mutuwar Femi Osibona, shugaban Kamfanin Fourscore Homes Limited, wanda ya rasu sakamakon rutsawar da rubzawar ginin yayi da shi. Osibona dai shi ne mamallakin kamfanin da ya gina benen mai hawa 21 da ya ruguje a unguwar Ikoyi dake Legas a ranar Litinin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu